Salva Kiir ya koka da shisshigin kasashe

Image caption Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya zargi dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da gudanar da aikinsu kamar wata gwamnati mai zaman kanta a kasar.

A jawabin da ya gabatar a gidan talabijin na kasa, Mr Kiir ya ce abinda ya rage wa majalisar kawai shi ne ta nada shugabanta tawagarta a kasar a matsayin shugaban kasar hadaka.

Shugaban ya kuma zargi kungiyoyin agaji da goyon bayan tsohon mataimakinsa Mr Riek Machar.

Rikicin da ya barke tsakanin shugaban kasar da tsohon mataimakinsa ya haddasa yakin basasa a Sudan ta Kudu.

Yanzu haka ana ci gaba da tattaunawar tsagaita wutar rikicin a kasar Ethiopia.

Karin bayani