'A tuhumi shugaba Assad da laifukan yaki'

Azabtar da jama'a a Syria
Image caption Azabtar da jama'a a Syria

Wakilan 'yan adawar Syria da suka isa Switzerland domin taron neman zaman lafiya sun bukaci da a gurfanar da Shugaba Assad da gwamnatinsa a gaban kotun duniya mai shari'ar manyan laifuka, dangane da wata sabuwar shaidar hotuna da aka fitar.

Wakilan 'yan adawar na mayar da martani ne game da wani rahoto da wasu masu gabatar da kara na kasashen duniya suka bayar, sakamakon wasu dubban hotunan da aka ce wani da ya sauya sheka ya yi satar fita da su daga Syria.

Hotunan sun nuna gawar fursunoni dubu 11, da yawa suna da shaidar da ke nuna an gana masu akuba.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana hotunan a matsayin abun damuwa, tana mai cewar sun jaddada muhimmancin samun wani sabon tsarin siyasa a Syria.

Tun farko kakakin gwamnatin Syriar, Bassam Abu Abdullah, ya gaya wa BBC cewar, rahoton wani makamin siyasa ne da aka hada don yin matsin lamba kan Shugaba Assad.