Iyalan Jami'an China sun sayi kadarori

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption China na kyamar cinhanci

Wasu bayanai da aka kwarmata sun ce iyalan manyan jami'an gwamnatin China sun kakkafa kamfanoni a wasu kasashen duniya domin kaucewa biyan haraji a kasar.

Rahoton da jaridun kasashen duniya suka wallafa, ciki har da jaridar Guardian ta Birtaniya, ya nuna cewa cikin mutanen da suka kafa kamfanonin har da surikin shugaban kasar Xi Jinping, da kuma dan tsohon Pirai Ministan kasar Wen Jiabao da kuma sirikinsa.

Yin hakan ba haram bane karkashin dokokin China, sai dai babu alamar da ke nuna cewa shugabannin na China suna da masaniya a wannan abun da suku yi.

Sai dai lamarin na iya kunyata shugaban kasar, Xi Jinping, wanda ya ci alwashin magance matsalar cin hanci da rashawa a kasar.

Karin bayani