Dakarun Ethiopia sun hade da AMISOM

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun kasar Ethiopia

Dakarun Ethiopia dake aiki a Somalia sun shiga cikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afurka wato Amisom.

Sun bayyana hakan ne a wani buki a garin Baidoa dake kudu maso yammacin kasar, wanda gari ne dake karkashin ikon dakarun Ethiopia.

Akwai dai dubban dakarun Ethiopia a tsakiya da kuma kudu maso yammacin Somalia.

Suna dai yaki ne da kungiyar Al Shabaab wacce take da alaka da kungiyar Al Qaeda.

Kafin dai wannan sanarwa Ethiopia ita ce kadai kasar da take da dakaru a Somalia da basa aiki karkashin rundunar kiyaye zaman lafiya ta kugiyar kasashen Afurka, wato AU da ake kira Amisom.

Karin bayani