Majalisa ta gayyaci speton 'yan sandan Nigeria

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Majalisar dattijai na kokarin ganin an kawo karshen matsala a jihar Rivers

Majalisar dattawan Nigeria ta gayyaci shugaban 'yan sandan kasar, Mohammed Abubakar, domin ya yi mata bayyani a kan yadda rundunarsa ke tinkarar rikicin siyasar da ya turnuke a jahar Rivers.

Matakin majalisar ya biyo bayan zargin harbin wani sanata da harsashin roba lokacin wata zanga-zangar lumana a birnin Fatakwal.

Jihar Rivers ta tsunduma cikin rikicin siyasa tun da gwamnan jihar ya koma jam'iyyar adawa ta APC, kuma 'yan siyasa na zargin 'yan sandan jihar da muzguna musu bisa umurnin wasu kusoshin gwamnati a Abuja.

Tun a ranar Talata ne 'yan majalisar wakilai suka bukaci a sauke sipeta-janar na 'yan sandan kasar, Muhammad Dahiru Abubakar, bisa zarginsa da gaza kawo karshen rikicin da ake fama da shi a jihar ta Rivers.

Karin bayani