Ma'aikatan lafiya na yajin aiki a Nigeria

Image caption Yajin aikin ma'akatan lafiya na jefa mutane cikin mummunan hali

A Nigeria, kungiyar ma'aikatan lafiya ta kasar ta fara wani yajin aiki na gargadi na kwanaki uku.

Kungiyar dai na zargin gwamnatin kasar ne da rashin mutunta hakkokin ma'aikata.

Wannan yajin aikin na zuwa ne bayan cikar wa'adin mako guda da kungiyar ta bai wa gwamnati kan ta magance matsalolin da suka dabaibaye harkar kula da lafiya a kasar.

Yajin aikin ma'akatan lafiya na jefa mutane cikin mummunan hali,lamarin da kan kai ga rasa rayuka.

Karin bayani