Ana zargin za a kai harin bom a Sochi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kafe fastocin Ruzanna Ibragimova a sassan Sochi.

'Yan sandan Rasha na neman wata mata da suke zargin ta na shirin kai harin kunar bakin wake a garin Sochi lokacin wasannin Olympics na hunturu.

An yi amannar matar, mai suna Ruzanna Ibragimova daga Dagestan a arewacin yankin Caucasus, matar wani dan gwagwarmayar Islama ne da ya mutu.

An dai rarraba fastocin matar da ake nema a dukan garin.

Shugaba Vladimir Putin ya sha alwashin tabbatar da tsaro lokacin wasannin Olympics din, kuma an zuba dubunnan 'yan sanda domin hana kai hari.

Karin bayani