An fara taron sasanta rikicin Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ban Ki Moon ya bude taron da ake wa lakabin Geneva II

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya bude taron kasa da kasa kan rikicin Syria, wanda ya kunshi tattaunawar gaba da gaba ta farko tsakanin gwamnatin Syria da 'yan tawaye.

Mr Ban ya ce rikicin ya raba kan 'yan Syria da kasashen duniya, kuma an sha wuya kafin a kai ga wannan matsayin.

Ya ce an yi asarar lokaci a baya, amma taron da ake gudanarwa a Switzerland da ma ce ta nuna amincewa da warware rikicin ta hanyar siyasa.

A ranar Juma'a ne ake sa ran fara tattaunawa kan tsagaita wuta da bude hanyoyin kai agaji.

Karin bayani