An kashe mutane biyu a rikicin Ukraine

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga sun shiga hatsari bayan da sabuwar dokar Ukraine ta halatta kama su.

An harbe mutane biyu a Ukraine lokacin arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga bayan kaddamar da sabuwar dokar da ta haramta zanga-zangar.

A dare na uku na rikicin, 'yan sanda sun karya shingayen da masu zanga-zangar suka dasa.

Sabuwar dokar ta bai wa gwamnatin damar daure mutane tsawon shekaru biyar bisa laifin toshe hanyar shiga gine-ginen hukuma sai dai matakin na shan suka daga masu zanga-zanga, Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Turai.

Yanzu haka dai an jikkata daruruwan mutane a Kiev, babban birnin Ukraine daga ranar Lahadi.