Birtaniya za ta sallami sojojinta 1,400

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsarin ba zai shafi dakarun dake Afghanistan ba

Gwamnatin Birtaniya ta ce kimanin sojoji dubu-daya-da-dari hudu ne za ta sallama daga aiki a matakan da kasar ke dauka na rage kudaden da take kashewa a fannin tsaro.

Amma kuma gwamnatin ta ce korar ba za ta shafi wadanda aka tura Afghanistan ba.

Tun shekarar 2010 ne rundunar sojin kasar keta rage ma'aikata a kokarinta na rage yawan dakarun kasar daga dubu dari zuwa dubu tamanin .

Wani Janar a dakarun Birtaniya ya ce wannan shi ne na karshe a cikin shirin rage yawan sojojin kasar.

Karin bayani