An kashe 'yan sanda biyar a Egypt

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sandan Egypt na cikin hatsari tun bayan juyin mulki

An kashe 'yan sanda biyar a Egypt a wani hari da aka kai shingen bincikensu da ke kudancin Cairo, babban birnin kasar.

An kuma jikkata wasu guda biyu, inda dayansu ya samu munanan raunuka a harin da aka kai a garin Beni Suef.

Maharan da ke bisa babura sun bude wuta ne a shingen binciken sannan su ka tsere.

Wata majiyar tsaro ta ce ana bincike a yankin domin lalubo maharan.

Akalla jami'an tsaro 250 aka kashe a Egypt tun bayan da sojoji su ka hambarar da mulkin shugaban kasa mai kishin Islama, Muhammad Morsi a watan Yulin da ya wuce.

Karin bayani