Mazaje 12 sun yi wa mace fyade a India

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fyade ya zama ruwan dare a India

Mazaje 12 sun yi wa wata mata fyade a jihar West Bengal da ke India bisa umarnin dattawan kauyensu wadanda ba su amince da soyayyar da ta ke yi da wani mutum da ba dan garinsu ba.

'Yan sanda sun kama mazajen da kuma dagacin kauyen.

Matar mai shekaru 20 na kwance a asibiti.

A baya bayan nan dai gwamnatin India ta tsaurara hukuncin da ake yi wa masu fyade bayan da aka samu adadin fyaden da su ka yi kaurin suna a kasar.

Karin bayani