'Sahihin zabe ne zai magance rikicin Syria'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kasa cimma matsaya a kan yadda za a magance rikicin Syria

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce sahihin zabe shi ne kawai maganin rikicin Syria.

Yayinda yake magana a wajen taron tattalin arziki na duniya da ke gudana a Davos, Shugaba Rouhani ya ce 'yan Syria ne kawai ya kamata su fayyace makomar kasar su ba tare da katsalandan daga kasashen yammacin duniya ba.

Kafin tafiyarsa zuwa Davos, Mr Rouhani ya ce tattaunawa a kan Syria da aka yi wa lakabi da 'Geneva Two' ba zai shawo kan matsalar ba, bayan da majalisar dinkin duniya ta janye gayyatar da ta yi wa kasarsa daga halartar taron.

Rouhani shi ne shugaban Iran na farko da ya halarci taron tattalin arzikin duniyar da ake yi shekara-shekara da manyan 'yan kasuwa, 'yan jarida da 'yan boko ke halarta.

Karin bayani