Hukumar Kwastam na rasa kudaden shiga

Ministar kudin Najeriya Ngozi Okwanjo Iwela Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Karamin Ministan kudin kasar Dr Yairma Lawal Ngama yace gwamnati ta janye kudin haraji ga manoman da ke son shigo da kayayyakin aikin noma kasar.

A Najeriya, wasu rahotanni na cewa kudin shigar da hukumar Kwastan ke samarwa a kasar ya ragu sakamakon rabewar da wasu 'yan kasar da kuma kamfanoni ke yi wajen shigar da kayan da gwamnati ta janye musu haraji.

Wasu alkaluma na cewa wannan ya sa gwamnati asarar sama da Naira tiriliyon guda cikin shekaru hudun da suka wuce.

Sai dai ma'aikatar kudin Najeriya ta ce ribar da kasar ke ci daga janye harajin ya fi karbarsa fa'ida.

Karamin ministan kudin Najeriyar Dr Yarima Lawan ya ce ba tara kudaden shiga ne aikin jami'an kwastam ba, ayyukansu sun hada da habaka cinikayyar da ake yi tsakanin kasa da kasa.

Ya ce: "A wannan habaka kasuwancin za a iya sanyawa wasu kayayyaki da ake shigo da su haraji, wasu kuma a janye musu harajin dan a samu saukin shigowa da su.

Misali idan manoma za su shigo da kayan aikin Noma babu batun haraji amma idan kayayyakin mutun ne na more rayuwa dole akwai haraji akansu."

Karin bayani