Bore ya hana sharia'r luwadi a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda sun tarwatsa masu bore kan a hukunta 'yan luwadi

Jami'an 'yan sandan Nigeria sun yi harbi a sama na tauna tsakuwa dan aya ta ji tsoro a jihar Bauchi da ke arewacin kasar, a lokacin da masu zanga-zanga su ka fito tare da bukatar a yankewa wasu da ake zargi 'yan luwadi ne su bakwai hukuncin kisa.

Ana dai tuhumar mazan ne a karkashin kotun shariar Musulunci da ke jihar, sai dai daruruwan matasa cikin fusata sun yi wa kotun tsinke tare da yin jifa da duwatsu a wajen kotu, abinda ya sa aka dakatar da zaman kotun.

Wannan dalili ya sa 'yan sanda tarwatsa masu zanga-zangar domin a samu damar ficewa da wadanda ake zargi daga kotun tare da mayar da su gidan kaso.

Luwadi da madigo dai haramun ne a dokokin addinin Musulunci da kuma na gwamnatin Nigeria, inda a baya bayan nan shugaban kasar ya rattaba hannu kan dokar da ta tsananta hukunci ga duk wanda aka samu da wadannan laifuka.

Karin bayani