An cimma tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Image caption Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Wakilan gwamnatin Sudan ta Kudu sun cimma yarjejeniya da 'yan tawaye a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

A karkashin yarjejeniyar, Sudan ta Kudu ta amince da daya daga cikin manyan bukatun 'yan tawayen kasar - wato sakin shugabannin siyasar su.

An kuma ce za a tsara yadda za a rika sa ido don ganin cewa yarjejeniyar ta dore.

Dubban mutane ne aka kashe a kasar tun bayan da fada ya barke tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawayen da suka juya masu baya.