An kama 'yan sanda hudu a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan Afrika ta Kudu sun yi kaurin suna kan zalunci

An kama 'yan sanda hudu a Afrika ta Kudu bisa kisan wani mai zanga-zanga ranar Alhamis.

Ana zargin 'yan sanda sun harbe Tshepo Babuseng mai shekaru 28 ne a lokacin zanga-zangar neman gidaje a Johannesburg.

Ana tuhumar daya daga cikin 'yan sandan da kisan kai, yayin da ake tuhumar ukun da "karye manufar shari'a".

An dakatar da 'yan sandan daga aiki kafin kammala shari'arsu.

Jami'an 'yan sandan Afrika ta Kudu sun yi kaurin suna kan cin zali da kuma amfani da harsashi wurin watsa taron masu zanga-zanga.

Karin bayani