Babban bom ya fashe a Cairo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bom din ya lalata gidan adana kayan tarihin Islama.

Wata mota makare da bama-bamai ta fashe a kofar babban ofishin 'yan sanda na Cairo, babban birnin Egypt, inda ta hallaka akalla mutane hudu tare da jikkata fiye da mutane 70.

Yayin da motocin agaji ke gaggawar zuwa wurin, ana iya ganin 'yan sanda su na kuka a bakin ginin.

Fashewar bom din ya kuma lalata gidan ajiye kayan tarihi na Musulunci mai makwabtaka da ofishin 'yan sandan.

Daga bisani kuma an samu wata fashewar kusa da tashar motoci ta gundumar Dokki, inda nan ma da dama su ka jikkata.

Hare-haren na zuwa ne ranar jajiberin bikin cikar shekaru uku da tada kayar bayan da ya hambarar da shugaban kasar Egypt, Hosni Mubarak.