Wasu bama-bamai sun fashe a Masar

Ma'aikatan aikin gaggawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ma'aikatan aikin gaggawa

Wani bamb da aka dana a wata mota ya fashe a kofar hedkwatar 'yan sanda a Alkhahira babban birnin kasar Masar.

Bamb din yayi sanadiyar mutuwar mutane 4 a yayin da wasu sama da 70 suka samu raunika.

Wasu rahotannin sun ce an yi yi harbi gabanin fashewar bamb din.

A yayin da ma'aikatan agajin gaggawa suka isa wurin da abun ya faru, an ga 'yan sanda suna kuka a kofar ginin.

Wani bomb din daban yayi sanadiyar mutuwar mutum guda.