Faransa ta kashe tsageru 11 a Timbuktu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Faransa a birnin Gao

Dakarun Faransa, sun kashe 'yan tada kayar baya 11 a wani samame da suka kai a birnin Timbuktu na arewacin Mali.

Kakakin sojin Faransa ya ce dakarun tsaro na sama su 100 ne suka shiga cikin samamen kuma sun lalata sansanonin 'yan tada kayar bayan.

A cewarsa, an kuma raunata sojin Faransa daya.

Faransa na ci gaba da kaddamar da ayyukanta na soji a Mali, tun a bara da ta kwato arewacin kasar daga hannun 'yan tawaye da masu kaifin kishin Islama.

Karin bayani