'Yan uwa Musulmi na iya shiga zabe a Masar

Image caption 'Yan uwa musulmi a Masar sun soki ikirarin Firaministan kasar

Pirai ministan rikon kwarya na Masar ya shaida wa BBC cewa magoya bayan haramtacciyyar kungiyar 'yan uwa Musulmi za su iya shiga wani bangare na zaben da za a gudanar a kasar; matukar za su tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce "Muna marhabin da dan kungiyar 'yan uwa musulmi in ya amince da sabon kundin tsarin mulkin, ya kuma ki amincewa da tashin hankali, ya amince da gwamnatin da babu addini a cikinta, ba hada addini da siyasa."

Hazeem Beblawi ya ce kuri'ar raba gardama da aka kada a watan da ya gabata game da sabon kundin tsarin mulkin kasar wani mataki ne na ciyar da dimokradiyya gaba, kuma hakan sharar fage ne ga zabukan shugaban kasa da 'yan majalisu watanni shida nan gaba.

Sai dai 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda ba a dade da ayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda ba na musanta zargin tada hankalin da ake mu su.

Karin bayani