Hambarar da Assad ba alheri ba ne—Rasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawayen Syria na bukatar a sauke Assad

Wani babban jami'in Rasha ya shaida wa BBC cewa a yanzu dai babu wani mutum da zai iya tafiyar da kasar Syria in ba Shugaba Bashar al-Assad ba.

Wadannan kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Syria da 'yan tawaye za su fara tattaunawa ranar Juma'a a Switzerland.

Mataimakin Pirai Ministan Rasha Arcady Vorkovich ya kuma ce tsige shugabannin kasashen Libya da Masar ba abin da ya kawo face tashin hankali; Rasha kuma na bukatar zaman lafiya ne.

Rasha dai ta ce rikicin Syria na fafutukar darewa kujerar shugabanci ne ba na kafa tsarin dimokradiyya ba.

Karin bayani