Gwamnatin Sokoto ta aurar da mata 125

Image caption Wasu daga cikin angwayen da aka yi wa aure

Gwamnatin jihar Sokoto dake arewacin Nigeria ta aurar da mata 125 a cikin shirinta na aurar da masu kananan karfi a jihar.

Gwamnatin jahar dai ta ce ta kashe kudi naira miliyan talatin domin aurar da matasan wadanda ba su da sukunin yin auren saboda tsadar da aure.

A jumlace mutane 250 ne za su amfani da wannan shirin, watau amare 125 da kuma angwaye 125.

Gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wammako ne zai kasance uban angwayen a yayinda Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III shi ne zai kasance uban amaren.

Gwamnatin jihar Kano ce dai ta soma bullo da irin wannan tsari na auren jama'a da yawa a lokaci guda a kasar, inda ta aurar da 'yan mata da zaurawa da fiye da 2,000.

Karin bayani