An fara sulhunta rikicin Syria

Image caption Al'ummar Syria na fatan tattaunawar za ta kawo tsagaita wuta nan take.

Bangarorin da ke yaki da juna a Syria za su fara tattaunawar sulhu a hukumance ranar Juma'a a karo na farko tun barkewar rikici shekaru uku da su ka wuce.

Wakilin gwamnati da na 'yan tawaye za su zauna a daki guda domin sauraron jawabin bude taro daga mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya, Lakhdar Brahimi, daga bisani su shiga dakuna daban-dabam inda za su rika tatttaunawar ta hannunsa.

Jami'an diplomasiyyar kasashen yamma da ke halartar taron sun ce babban burinsu shi ne su tabbatar babu wani bangare da ya fice daga wurin taron.

Har yanzu dai akwai kwakkwaran bambanci game da makomar shugaba Assad.

Mataimakin Pirai Ministan Rasha, Arcady Dvorkovich ya shaida wa BBC cewa a yanzu babu wanda zai iya tafiyar da Syria in ban da Mr Assad.

Karin bayani