Bankin duniya zai tallafa wa Burma

Shugaban Bankin  Duniya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Bankin Duniya

Shugaban bankin duniya Dr Young Kim ya ce bankin zai tallafa wa kasar Burma ko Myanmar da dala biliyan biyu.

Ya ce za a yi amfani da rabin kudin ne wajen samar da wutar lantarki sannan kuma za a yi amfani da dala miliyan dari biyu wajen aikin kiwon lafiya.

Yanzu haka kashi 70 cikin dari na jama'ar kasar ne ke fama da karancin wutar lantarki.