An fara ganawa tsakanin gwamnatin Syria da 'yan adawa

Wakilan tattaunawa kan Syria a Geneva Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wakilan tattaunawa kan Syria a Geneva

Wakilan gwamnatin Syria suna ganawa kai tsaye a karon farko da shugabannin 'yan adawa a daki daya a taron sulhun dake ke gudana a Geneva.

Sai dai basu cewa juna komai ba a zaman farko da suka yi.

Babban mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya Lakhdar Brahimi, ya ce suna sane cewa "tattaunawar zata kasance mai sarkakiya."

Idan anjima ne ake saran za a ci gaba da tattaunawar.

Ana saran zasu maida hankali ne akan batun musayar fursunoni da kuma kai kayan agaji ga wadanda fadan ya jikkata.

'Yan tawayen sun ce zasu bukaci tsagaita wuta a garin Homs.

Bangarorin biyu sun ce zasu fayyace yadda suke ganin za a warware rikicin kasar.