Ana ci gaba da zargin juna a Sudan ta Kudu

Mayakan 'yan tawaye a Sudan ta Kudu
Image caption Mayakan 'yan tawaye a Sudan ta Kudu

Gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye sun ci gaba da zargin juna da rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita fadan da suke yi, wadda ta fara aiki ranar Juma'ar da ta wuce.

Wani kakakin rundunar 'yan tawayen ya ce sojojin gwamnati sun kai masu hari a wurare da dama.

Sai dai kuma gwamnatin ta musanta hakan.

A nata bangaren , gwamnatin na cewa 'yan tawayen ne suka saba yarjejeniyar.