Wakilan rikicin Syria na ci gaba da ganawa

Lakhdar Brahimi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lakhdar Brahimi

A karshen yini na biyu a taron kawo karshen rikicin Syria da ake yi a Geneva, Mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya, Lahkdar Brahimi ya ce an samu ci gaba, musamman ma a kan makomar wadanda ke cikin garin Homs.

Ya ce sun tafka mahawara a kan Homs kuma yanzusuna fata sun kusa samun mafita ga farar hular da ke garin.

Wakilan gwamnati sun yi alkawarin zasu saki mata da yaran da fadan ya rutsa da su.

Sai dai sun ce suna bukatar jerin sunayen sauran mutanen da ke garin, kafun a sako su.

Ya zuwa ranar Litinin, mata da yaran zasu iya barin garin.

Ya kara da cewa an tabo batun musayar fursononi sai dai ba a tsaida da magana ba.