An harbe wani jagoran adawa a Bangkok

Masu zanga zangar adawa a Thailand Hakkin mallakar hoto REUTERS

An hallaka daya daga cikin shugabannin wata kungiyar adawa a Thailand, a wata arangama da magoya bayan gwamnati , a Bangkok babban birnin kasar.

An harbe mutumin ne mai suna Suthin Taratin lokacin da yake jawabi a wurin wani gangami, kuma ya cika ne a asibiti.

Masu zanga zangar na adawa ne da zaben sharar fagen da ake yi ne yanzu, gabanin zabukan gama -gari da aka shirya yi a makon gobe.

An samu hatsaniya a wasu runfunan zabe a kasar inda wasu suka ce an hanasu kada kuri'a.

Masu zanga zangar na so ne a yi garambawul ga tsarin siyasar kasar kafin a yi zabe.