CAR: An kafa gwamnati

Praministan jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Andre Nzapayeke, ya kafa gwamnatin wucin gadi da ta hada da mata bakwai.

A ranar Asabar ce sabuwar shugabar kasar ta riko, Catherine Samba-Panza ta nada shi a matsayin Praminista.

Ta dai sha alwashin kawo karshen rikicin addinin da kasar ke fama da shi.

Kwamishinar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya, Navi Pillay, ta ce a 'yan kwanakin nan yanayin tsaro a jamhuriyar Afirka ta tsakiyar ya tabarbare

Ta kuma ce, musamman Musulmi sun sami kansu cikin halin kaka-nika yi.