Masar: Soja sun ce Al-Sisi ya tsaya takara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Field Marshal Al Sisi

Majalisar ƙoli ta soja a Masar ta ce, ya kamata shugaban sojojin, kuma ministan tsaro, Abdel FAttah al-Sisi, ya saurari abinda ta ce, kiraye-kirayen jama'a na ya tsaya takarar shugabancin ƙasa.

Gidan talabijin din Masar ya gabatar da wata sanarwa a kan takarar Al-Sisi.

Sanarwar ta ce, Field-Marshal Al-Sisi ya gode wa shugabannin sojojin, kan yadda suka bashi izinin amsa kiran da jama'a suka yi masa.

Nan da 'yan kwanaki ake sa ran zai fito ya bayyana takararsa.

Masu aiko da rahotanni suka ce, Field Marshal al-Sisi ne ake jin zai lashe zaben da za a yi a tsakiyar watan Afrilu ba tare da zufa ba.