Taron Bankin Musulunci a Senegal

Wani bankin Musulunci Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani bankin Musulunci

Bankin Musulunci na raya kasashen duniya ya shirya taron nazarin ayyukansa da za a fara ranar Litinin a Dakar, babban birnin Senegal.

Ana sa ran wakilai daga kasashen Afrika 17 za su halarci taron inda za su yi nazari game da irin rawar da bankin ke taka wa da kuma kalubalen da yake fuskanta a wani bangare na bikin cika shekaru 40 da kafa bankin.

Za a yi waiwaye ne kan wane irin ci gaba bankin ya kawo a cikin shekaru 40 da suka wuce kuma wadanne abubuwa ya kamata ya mai da hankali a cikin shekaru masu zuwa, da kuma kalubalen da ake fuskanta.

Bankin ya bayar da gudumawa a kasashen Afirka da dama da suka hada da habaka tsarin banki na addinin musulunci, gina makarantu, madatsun ruwa, filayen jirgen sama da sauran abubuwa na raya kasa.