Rikicin addini na karuwa a Malaysia

Image caption Ana takaddama game da amfani da sunan Allah a Malaysia

'Yan sanda a Malaysia sun tsaurara tsaro a coci-cocin da ke jihar Penang bayan da aka sa wa daya daga cikinsu wuta.

Harin ya sa an shiga damuwa game da sabani tsakanin Kirista da Musulmi masu rinjaye, dangane da amfanin da wadanda ba Musulmi ba ke yi da sunan "Allah".

An daura wasu manyan tutoci dauke da kalaman "Allah mai girma, Yesu dan Allah ne" a coci uku da ke Penang, ciki har da wanda aka kai wa harin.

Shugabannin cocin dai sun ce ba su suka daura tutocin ba amma wakilin BBC ya ce ana ganin harin a matsayin martani game da amfani da sunan "Allah".

A watan Oktoban da ya gabata ne wata kotu ta zartar da hukuncin cewa Musulmi ne kawai za su iya kiran Ubangiji da sunan "Allah".