Taron kungiyar gidajen rediyoyi na Afirka a Yaounde

Taswirar kasar Kamaru
Image caption Taswirar kasar Kamaru

Shugabannin wasu gidajen rediyoyi karkashin kungiyar gidajen rediyoyi na Afrika naa halartar wani taro a birnin Yaounde na Jumhuriyar Kamaru.

Mahalarta taron dai za su tattauna batutuwan da suka shafi sauya kayan aikinsu na yada labarai ne zuwa na zamani wato "Analogue" zuwa "digital" daga shekara ta 2015.

Za kuma a yi kokarin lalabo hanyoyin magance matsalar da gidajen rediyoyin ke fuskanta wurin watsa manyan gasar wasanni kamar wasan neman cin kollon kafa na duniya da kuma ma na Afrika.

Matsalolin sune hukumomin dake kula da wasannan kan baiwa wasu 'yan kwangila damar nuna wasannin, maimakon masu kafofin watsa labarai kai tsaye da kan aza musu biyan wasu kudade kafin su watsa.