Ba zamu bari a zare mana ido ba — El-Rufai

Image caption El-Rufai na caccakar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan

Mataimakin Sakataren Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria, Malam Nasir El-Rufa'i ya ce ba zasu bari gwamnatin kasar ta zare musu ido ba ta hanyar yi musu barazana.

A shafinsa na Twitter, tsohon ministan Abujan, ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin razanar dasu don ta samu sukunin gudanar da magudin zabe a kasar a shekara ta 2015.

Ya caccaki gwamnatin ne kwana guda bayan da ya amsa gayyatar hukumar tsaro ta farin kaya a Nigeria, SSSinda ya kwashe sa'o'i 15 a hannunta yana amsa tambayoyi.

Hukumar ta SSS ta gayyaci Malam El-Rufa'i ne domin amsa tambayoyi game da kalamin da aka rawaito ya ce za a zubar da jini a Nigeria matukar ba a yi adalci a zabukan 2015 ba.

El-Rufa'in dai ya ce wannan zan ce ba ingiza tashin hankali ba ne, illa tunatarwa game da irin rikice-rikicen da su ka biyo bayan zabubbukan da aka gudanar a kasar a baya.

Sai dai jam'iyyar ta APC ta yi Allah-wadai da gayyatar ta SSS, inda ta yi zargin cewa gwamnati na amfani da jami'an tsaro da nufin karya-lagon 'yan adawa.

Karin bayani