Mladic da Karadzic sun bayyana gaban kotu

Image caption Su biyun ake zargi da kashe musulmai fiye da 7,500

Mutane biyu daga cikin masu fada-a-ji a lokacin yakin Bosnia na shekarun 1990, sun bayyana a lokaci guda a kotun duniya da ke Hague amma an tashi baram-baran.

Mutumin da a da ake wa lakabi da 'mahaucin Bosnia', watau tsohon kwamanda Ratko Mladic, ya bayyana a kotun a matsayin shaidar wanda ake tuhuma.

To amma ya ki ya amsa tambayoyi daga tsohon jagoran Sabiyawan Bosnia, Radovan Karadzic.

Ratko Mladic ya ce, kotun ta 'shaidan' ce, kuma akwai yiwuwar zai yi rashin lafiya idan aka matsa masa sosai.

Tun farko kuma ya ki yayi magana saboda ba ya sanye da hakoransa na likita.

An dai dage sauraron karar.

Musulmi fiye da 7,500 ne aka kashe sakamakon yakin.

Karin bayani