An sake kama dan jarida a Nijar

Image caption Brigi Rafini, Pirai ministan Nijar.

Mahukunta a jamhuriyar Nijar sun kama wani dan jarida tare da 'ya'yan kungiyar farar hula guda biyu bisa zargin yi wa jami'an gwamnati kazafi.

A yammacin Litinin ne hukumar 'yan sanda masu binciken manyan laifuffuka ta PJ ta kama Zakari Adamu na gidan talabijin Canal 3 da Malam Usman Dambaji na kungiyar RENJED da kuma Malam Nayusa Jimrau na kungiyar MPCR.

Gwamnatin na zarginsu ne da yi wa wasu jami'anta kazafin sun tara kazaman kudade cikin dan takaitaccen lokaci, a yayin wata muhawara a gidan talbijin na Canal 3.

Ga alama dai mutanen uku na daga cikin kamen da ministan shari'a ya ce gwamnatin za ta yi domin binciken wasu kalamai mara sa dadi da ya ce an yi wa hukumomin kasar.

A ranar Litinin ne dai mahukuntan Nijar su ka saki wasu 'yan jarida biyu da aka kama bisa zargin bai wa 'yan adawa damar sukar gwamnati, bayan da su ka yi kwanaki uku a tsare.

Karin bayani