"Masarautar Ingila na barnar kudi"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwamitin na son a kara lokutan bude wa maziyarta fadar Buckingham domin samar da kudin shiga.

Wani kwamitin majalisar dokokin Birtaniya, ya soki yawan kudaden da masauratar kasar ke batar wa a duk shekara.

A bara dai an kashe wa masauratar $50 miliyan (N8.5 biliyan) in aka dauke abin da aka batar da sunan tsaro.

Shugabar kwamitin Margaret Hodge ta ce ya kamata masarautar ta sallami wasu daga cikin fadawanta sannan kuma ta kara adadin kudin shigar da ta ke samar wa.

Ms Hodge ta bukaci a kara yawan lokutan da ke bude wa maziyarta fadar Buckingham domin samar da kudin shiga.

Jami'an fadar sarauniyar dai sun ce kwalliya na biyan kudin sabulu.