Firaministan Ukraine ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Azarov ya yi murabus don baiwa 'yan adawa damar shiga cikin gwamnati

Shugaban Ukraine Viktor Yanukovych ya amince da murabus din Firaministan kasar, Mykola Azarov da daukacin majalisar ministoci.

Amma kuma ya bukace su cigaba da zama kan mukamansu zuwa lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati.

Ita kuma majalisar dokokin Ukraine ta kada kuri'ar soke dokar nan da aka zartar kwanan baya dake haramta zanga-zanga, dokar da ta tunzura tarzomar da ake yi a kasar.

Dokar ta kuma haramta mamaye gine-ginen gwamnati da kuma rufe fuska yayin zanga-zanga.

Shugaba Victor Yanukovych ya amince da soke dokar bayan tattaunawa da shugabannin masu yi wa gwamnati bore.

Tashin hankali ya barke yayin da aka fara aiwatar da dokokin a farkon wannan watan.

Karin bayani