Ba mu bi Shekarau ba - 'Yan Majalisa

Image caption Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila.

'Yan majalisar wakilan Nigeria daga jihar Kano wadanda aka zaba a rusassun jam'iyyun ANPP da CPC sun ce ba tare da su tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau ya koma PDP ba.

Jagoran 'yan majalisar kuma mataimakin shugaban mara sa rinjaye a majalisar wakilai, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce: "Muna nan a APC kuma ba za mau sauya sheka zuwa wata jam'iyya ba."

Kawu Sumaila, wanda ya jagoranci 'yan majalisar 10 ya shaida wa manema labarai cewa sun dade su na gwagwarmayar ceto al'umma daga abin da ya kira "rashin adalci" na mulkin PDP.

Sanarwar ta su ta biyo bayan sauya shekar da tsohon jagoran APC a jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi zuwa PDP a ranar Laraba.

Karin bayani