Boko Haram: Mutane 83 aka kashe a Kawuri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Ana cigaba da samun karin bayanai dangane da harin da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kauyen Kawuri dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno a Nigeria.

Alkaluman baya-bayan nan na cewa, mutane 83 ne aka hallaka sakamakon harin, yayin da wadanda suka tsira suke jinya a asibiti.

Haka kuma, a lokacin harin an bankawa gidajen kauyen baki daya da masallatai biyar.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya zayarci kauyen Kawuri tare da wasu 'yan tawagarsa don duba irin barnar da aka yi inda ya bada tallafin kayayyakin abinci da al'ummar da aka kaiwa hari.

Sakataren gwamnatin jihar Borno, Ambasada Baba Ahmed Jidda ya shaidawa BBC cewar gwamna Shettima ya ce gwamnati za ta tallafawa wadanda lamarin ya shafa da kudade da kuma sake gina musu gidajensu.

Karin bayani