Nigeria ta kaddamar da jirgin ruwan yaki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daya daga cikin jiragen ruwan Nigeria

A wata alama ta karuwar mu'amalar China da Afrika a ranar litinin an kaddamar da wani jirgin ruwan yaki na farko da China ta taba kerawa Najeriya a Birnin Wuhan na China tare da shagali.

Kamar dai yadda kafofin watsa labaran China su ka ruwaito, uwar gidan shugaban Najeriya na daga cikin manyan bakin da suka halarci bukin.

Hotunan sun nuna wasu baki na duba babban injin jirgin ruwan yakin kafin a kaddamar da jirgin ruwan yakin mai suna NNS F91 da aka yi wa kwalliya zuwa tashar ruwa.

Jirgin mai tsawon mita 95 da fadin mita 12 da kuma nauyin tan dubu daya da 600, samfarin P18N zai kasance kari ga sojin ruwan Najeriya.

Zai kasance da karfin amfani da bindigogi 5 sannan za a iya tayar da helikwabta daga saman jirgin ruwan yakin, wanda zai iya yin aiki a cikin teku har tsawon kwanaki 24 jere ba tare da tsayawa ba.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya amince da sayen manyan jiragen ruwan yakin 2 daga China a 2012 a wani kokari na karfafa sintiri a yankin tekun Gulf game da hare-haren yan fashin teku da kuma kare dinbin rijiyoyin mai a yankin.

Karin bayani