Obama zai daidaita albashin maza da mata

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama ya koka da gibi tsakanin maza da mata da kuma mai kudi da talaka.

Shugaban Amurka Barak Obama ya sha alwashin daidaita albashin maza da mata masu aiki iri daya a fadin kasar.

Mr Obama ya kuma koka da wawakeken gibin da ya ce ya na karuwa tsakanin masu kudi da talakawan Amurka, a jawabin da ya gabatar a zauren majalisar dokokin kasar.

Ya ce a yanzu tauraron Amurka na haskawa har 'yan kasuwa sun gwammace zuba jari a kasar fiye da China.

Don haka ya ce zai dauki matakan tabbatar da bunkasar arzikin Amurka ta amfani daukacin 'yan kasar ta hanyar hada kai da 'yan majalisar dokokin duk da bambancin siyasar da ke tsakaninsu.

Karin bayani