Jam'iyyar APC ta samu karin sanatoci 11

Image caption Shugaban majalaisar bai karanta takardar ba

'Yan majalisar dattawan Nigeria guda 11 sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

'Yan majalisar dattawan sun bayyana ficewarsu daga PDP ne a zauren majalisar, lokacin da suka mikawa shugabanta, David Mark, takardar fita daga PDP.

'Yan majalisar su ne: Abdullahi Adamu da Bindao Jibrin, Aisha Alhassan, Danjuma Goje, Bukola Saraki da Mohammed Ali Ndume da Umaru Dahiru.

Sauran su ne: Magnus Ngei Abe da Wilson Asinobi Ake da Mohammed Shaba Lafiaji da kuma Ibrahim Abdullahi Gobir

Sai dai David Mark bai karanta takardar kamar yadda al'adar majalisar ta bukaci ya yi ba.

A baya dai 'yan majalisar wakilar 37 sun fice daga jam'iyyar ta PDP zuwa APC.

Karin bayani