Shekarau ya koma jam'iyyar PDP

Image caption Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, wanda ya yi wa jam'iyyar ANPP takarar shugabancin kasa a shekarar 2011 Malam Ibrahim Shekarau, ya fice daga jam'iyyar APC inda ya koma jam'iyyar PDP.

Malam Shekarau dai ya koma jam'iyyar ta PDP ne da magoya bayansa a wani taron masu ruwa da tsaki na tsohuwar jam'iyyar ANPP inda suka yanke hukuncin tafiya PDP.

Malam Shekarau dai shi ne tsohon gwamna na biyu da ya fice daga APC inda suka shiga PDP sakamakon rigingimun cikin gida a APC bayan kafuwar ta.

Karin bayani