Nigeria da Niger ne koma baya a ilimi

Nigeria tafi kowacce kasa a duniya yawan yaran da ba sa makarantar firamare yayin da yaran Nijar su ne suka fi na ko'ina karancin koyar ilimi a makarantunsu.

Wannan bayani na kunshe ne cikin rahoton Hukumar Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya (unesco), wanda ta fitar ranar Laraba a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Rahoton ya ce sai nan da shekaru 70 za a cimma kudirin tabbatar da kowanne yaro a duniya ya samu ilimin firamare maimakon shekarar 2015 da aka sa gaba.

A cewar rahoton akwai yara miliyan 57 da ba sa makarantar firamare kuma sai nan da shekarar 2086 kafin baki dayan yara mata a kauyukan Afrika su shiga makaranta.

Rage tallafi

Mawallafiyar rahoton, Pauline Rose ta ce a kasashe matalauta, cikin duk kan matasa hudu, akwai daya da ba zai iya karanta jimla guda ba, abinda ke tasiri ga bunkasar tattalin arziki da kuma dorewar mulkin dimokradiyya.

Rahoton na Unesco dai nazari ne na shekara-shekara game da aiwatar da alkawurran bunkasa samar da ilimi da kasashen duniya su ka yi.

Sai dai ya bayyana cewa kasashen duniya sun rage tallafin da su ke bai wa kasashe masu tasowa ta fannin ilimi.

Kasar da tafi kowacce samun tallafin ilimi ita ce China - wacce ake bai wa agajin da ya nunka na Chad sau 77.

Duk da haka wasu kasashe irin su India, Vietnam, Ethiopia da Tanzania sun samu gagarumar nasara wurin samar da ilimi ga yaransu.

Yammacin Afrika

Idan aka fi samun matsala shi ne a kasashen Afrika da ke kudu da Sahara, musamman ma yammacin Afrika.

A Nigeria, adadin yara da ba sa makarantar firamare karuwa ya ke maimakon raguwa.

Kusan rabin wadanda su ka daina makarantar kuma tashin hankali da rikici ne su ka hana su.

Rahoton ya kuma nuna yara maza sun fi mata samun damar shiga makaranta a kasashen yankin.

Sai dai ga wadanda ke makarantar ma, ingancin ilimin babu tabbas don kuwa akwai yara miliyan 130 a duniya wadanda ba su iya karatu da rubutu ba duk da cewa sun yi makarantar firamare.

Ingancin koyarwa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahoton ya kiyasta cewa a wasu kasashen rabin abinda ake batar wa ilimi asara ne saboda rashin ingancin ilimin da ake samar wa.

Kan haka ne rahoton ya bukaci a kara ingancin koyarwa musamman ma a yammacin Afrika inda malamai ke fama da karancin albashi, aikin wucin gadi da kuma karancin horo.

Haka kuma ana bukatar karin akalla malaman firamare miliyan 1.6 a fadin duniya.

Tuni dai shugabannin duniya su ka fara tsara matakan da za su dauka na samar da ilimi bayan shekarar 2015.

A cewar rahoton, wajibi ne sababbin matakan su hada da inganta ilimin da ake samar wa da kuma malaman da ke ba da shi.