Gwamnatin Nigeria ta soki Jam'iyyar APC

Hakkin mallakar hoto nigeria villa
Image caption Gwamnatin Najeriya ta soki APC

Gwamnatin Nigeria ta soki babbar jam'iyyar adawa, ta APC dangane da umurnin da ta bai wa 'ya'yanta da ke majalisar dokokin kasar.

Jami'yyar dai ta umarce su da su ki amincewa da duk wani kudiri ko bukatar da ta fito daga bangaren zartarwa, ciki har da kudirin kasafin kudin bana.

Bangaren shugaban kasar ya bayyana matakin da cewa bakar adawa ce da za ta iya cutar da al'ummar kasar baki daya.

Ministan yada labarai Mr Labaran Maku ya ce daukar irin wannan mataki bai kamata ba.

Karin bayani