Kasashen AU na taro kan rikice-rikice

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce dole a hada kai don samar da zaman lafiya a Afrika.

Kungiyar kasashen Afrika, AU, na gudanar da taro a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia inda batun rikicin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Sudan ta Kudu za su mamaye tattaunawar.

A jawabinta na bude taro, shugabar kungiyar, Nkosazana-Dlamini Zuma ta shaida wa kasashen nahiyar 54 cewa akwai bukatar su hada kai domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dai ta shiga rikici ne bayan da 'yan tawaye su ka hambarar da gwamnati watanni 10 da su ka wuce.

A kasar Sudan ta Kudu mai makwabtaka kuwa, a makon jiya aka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta sai dai ana ci gaba da tafka arangama tsakanin dakarun soji da 'yan tawaye.

An dai kashe dubunnan mutane a rikice-rikicen.