Za a kashe dillalan makamai a Bangladesh

Hakkin mallakar hoto focusbangla
Image caption Motiur Rahman Nizami ya ce zai daukaka kara.

Wata kotu a Bangladesh ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane 14 da aka samu da laifin safarar makamai zuwa ga kungiyar 'yan tawaye a kasar India mai makwabtaka.

Cikin wadanda aka yanke wa hukuncin har da wani jagoran jam'iyyar Jamaat-e-Islami, Motiur Rahman Nizami da kuma wani tsohon ministan harkokin cikin gida.

An samu mutanen ne da laifin fasa kwaurin bindigogi fiye da dubu hudu tare da wasu kayayyakin aikin soji a cikin kwale kwale a shekarar 2004.

Sun fitar da makaman ne zuwa ga masu tada kayar baya a jihar Assam da ke arewa maso gabashin India.

Mr Nizami dai ya ce zai daukaka kara.