Maneman aure sun yi caa kan 'yar luwadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gigi Chao (a dama) tare da matar da ta aura.

'Yar luwadin nan da babanta hamshakin dan kasuwar Hong Kong ya yi tayin Naira biliyan 11 ga duk namijin da ya aure ta, ta shaida wa BBC cewa manema sun yi mata yawa.

Gigi Chao, wacce ta auri abokiyar zamanta, ta aike da budaddiyar wasika ga mahaifinta inda ta bukaci ya daina kokarin sama mata miji.

Ta ce maza sun yi caa akanta tun da babanta Cecil Chao ya yi tayin ba da makudan kudi.

A makon jiya dai baban ya nunka kyautar zuwa Naira biliyan 22 ga duk namijin da ya yi nasarar shawo kan 'yarsa ta aure shi.